An bayyana Kungiyar ‘yan uwa musulmi ta IMN da alhakin kisan DCP Umar Usman, mataimakin yan sanda a birnin tarayyar Abuja.
DABO FM ta binciko cewa; duk dai a yayin gudanar da zanga-zangar, yan Shi’a sun kone motocin hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA kamar yacce duk Jaridun suka tabbatar.

A cikin makon da muke ciki dai shugaban ‘yan sandan Najeriya, ya haramta dukkanin wata zanga-zanga a wasu titunan birnin tarayyar Abuja.
Sai dai DABO FM ta tabbatar da bijirewa umarnin rundunar yan sandan da kungiyar ta Shi’a tayi bisa hujjarsu ta cewa “Su ba zanga-zanga sukeyi ba.”
A ranar Litinin dai kungiyar ta cigaba da gudanar da zanga-zangarta domin neman saki shugabanta dake tsare a hannun gwamnati bisa umarnin Kotu.
