Yanzu-yanzu: An kara tsawaita dokar kulle a Kano na tsawon sati 2

by Dabo Online
0 comments

Kwamitin yaki da cutar Koronabairas na kasa, ya kara tsawaita dokar kulle a jihar Kano ta tsawon mako 2.

Shugaban kwamitin, Boss Mustapha ne ya sanar da haka a yau Litinin yayin bayanai game da cutar Kwabid19 da kwamitin ya saba yi kullin a birnin Abuja.

DABO FM ta tattara cewar tin dai ranar 16 ga watan Afrilu, gwamnan Kano, Dr Ganduje ya fara sanya dokar hana fita a jihar na tsawon mako guda.

Bayan fargaba da karuwar masu dauke da cutar Kwabid19 suka yawaita a Kano, ranar 27 ga watan Afrilu, shugaba Buhari ya sanya sabuwar dokar zaman gidan na tsawon makonni biyu domin bai wa ma’aikatan lafiya damar bincike.

A bisa kiduddugar 17 ga watan Mayu, mutane 825 ne suka kamu da cutar a jihar Kano tare da samun mutuwar mutum 36.

Haka zalika mutum an sallami mutum 112, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.

Cikakken bayanin na zuwa…

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00