Zamani Riga: Me duniyar Kannywood take ciki a Yau da nasarorinta?

dakikun karantawa
Yan Matan Kannywood, dabofm

Ahmad Muhammad Nass.

Sana’ar fim na daya daga cikin sanao’in da suka shahara kuma ta samu karbuwa tsakanin al’umomin yankuna da dama a duniya.

Sana’ar Fim sana’a ce da ma’abotanta da gungun masana ke dangatawa da wa’azantarwa, nishadantawa, da ilimantarwa.

Tun bayan shigo da wannan sana’a arewacin kasar nan da zamani ya yi, masu sha’awarta suka karbeta hannu bibbiyu, ta hanyar gudanar da wasan dabe har takai ga ana shirya irin wadannan wasannin dirama a gidajen talabijin domin jaddada wadancan ginshikai da aka kirkikiri wannan sana’a.

Bayan zamani mai tsawo da aka dauka ana gudanar da wannan sana’a, tin a shekarun baya an samu kafuwar kamfanoni da suke shiyar fina -finai a harshen Hausa a karkashin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.

A farkon wadancan shekaru masu kallo na yaba kokarin masu shirya fina-finai, sai dai zuwa yanzu korafe-korafe sun yawaita da yadda zamani ya kawo mu lokacin da masu wannan sana’a suka kauda kai daga fadakarwa da ilimantarwa tare da nishadantawa da suka dace da koyarwar addini da al’adar da muka taso cikinta.

Wasu daga cikin masu wannan sana’a sun tasirantu da yada al’adun da suke na wasu ne, mai makon yin amfani da damar da suka samu su fadakar da kuma nishadantar da masu kallo daidai da koyarwar addininmu, ta gefe guda su yadawa duniya kwayawawan al’adun yankin da muka fito, kamar yanda suma takwarorinsu na sassan duniya suke martaba addini da al’ada da nuni da muhimman abubuwan da kasashensu suka mallaka.

Kasancewar masu wadannan sana’a yan’uwanmu ne a addinance da al’adance, don haka suna da hakkin yi masu matashiya da yanda ya kamata su tsarkakake sana’arsu daidai da addini da al’adar mallam Bahause ta yanda za’a magance tabarbarewar tarbiyar da ake zarginsu da kawowa cikin al’umarmu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog