Home LabaraiYanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben kujerar Abdulmumin Kofa da tazarar kuri’u 35,094

Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben kujerar Abdulmumin Kofa da tazarar kuri’u 35,094

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Tsohon dan majalisan wakilan tarayya, AbdulMumini Jibrin, ya fadi ba nauyi a zaben mai-mai da aka gudanar a mazabar Kiru/Bebeji na jihar Kano.

Majiyar Dabo FM ta bayyana Jibrin wanda yake dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya sha kasa hannun abokin hamayyarsa Alhaji Ali Datti Yako, na Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar 25 ga Junairu, 2020.

Baturen zaben, Farfesa Abdullahi Arabi, ya ce Ali Datti ya samu kuri’u 48,641 yayinda AbdulMumini Jibrin ya samu kuri’u 13,507. Kamar yadda Legit.NG ta rawaito.

Wannan ya biyo bayan fito na fito da yayi da jam’iyyar tasa, wanda dama tini dattijan Jam’iyyar sun shirya masa gadar zare.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00