(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
/

Zaben2019: Najeriya zatayi asarar biliyan 140, dalilin dage zabe

Karatun minti 1

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Najeriya (NANTs), Mr Ken Ukaoha, yace Najeriya zatayi asarar naira biliyan 140 saboda dalilin dage zaben shugaban kasar da akayi wanda aka shirya gudanarwa yau Asabar.


Yace yau kusan duka ‘yan kasuwar Najeriya basu bude shagunan kasuwancinsu ba.
”Manoma, masu aikin kamfani da ma’aikatan gwamnati duka suna hutu balle mu ‘yan kasuwa.

“
Ya kara da cewa, dole ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kara shiri domin gudun kara tafka wannan gagarumar asara.
Yayi kira da manoma da duk yan kasuwa, dasu tabbatar da cewa sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’arsu a ranar 23 ga watan Fabarairun 2019.


A daren yau ne hukumar zabe ta dage gudanar da zaben shugaban kasa, ‘yan majalissar dattijai da wakilai zuwa 23 ga wata.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog