Labarai

Shugaban INEC yayi murabus?

Biyo bayan dage babban zabe da hukumar INEC tayi a yau Asabar, lamarin ya jawo cece kuce a tsakanin al’ummar Najeriya.


Mutane musamman matasa sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin hukumar, hakan yasa wasu na ganin hukumar bata shirya gabatar da ingantaccen zabe ba.


Rashin yadda da dalilan da hukumar INEC ta bayar, yasa wasu cire rai da yin zaben, suna ganin koda ma sunyi zaben, bazai zamto na gaskiya ba.


Anya Hukumar INEC ta shirya gabatar da zaben?
Itace tambayar dake ta yawo a zukatan al’ummar Najeriya.

Ra’ayoyin wasu matasa.
“Hukumar INEC ta dade tana shirin gudanar da wannan zaben, gaskiya mudai ta bamu kunya matuka, kuma hakan ya nuna hukumar bazata iya gudanar da nagartaccen zabe ba.”

“Yakamata shugaban hukumar yayi murabus, domin ya nuna gazawarshi a fili.”

Yaya manyan jam’iun Najeriya suke kallon dagawar zaben?


 A nasu bangaren, manyan jami’un kasar, APC da PDP sun bayyana rashin jin dadinsu ga al’amarin.
Kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari yace “Lallai bamuji dadin dage wannan zabe ba, kuma muna fatan bashida alaka da shirin magudin jami’iyyar PDP ke son yi.”

Suma a nasu bangaren, jami’iyyar PDP ta hannun shugabanta Mr. Scandalous, tace “Dage zabe yanada alaka da shirin shugaba Muhammad Buhari na ganin ya sake darewa kan karagar mulkin kasar”

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben Gwamna: Matasa sunyi kwanan tsaye a ofisoshin tattara sakamakon zabe

Dangalan Muhammad Aliyu

Kano: Mutane 176 ne suka rasa ransu sakamakon hadarin jirgin sama a rana irin ta yau

Muhammad Isma’il Makama

Zaben2019: Ba’a kama wani matashi ‘dan PDP da bugaggen sakamakon zabe ba, labarin bogi ne – Hukumar ‘Yan sanda

Dabo Online

Abuja: Malam Shekarau ya karbi shedar zama sanatan Kano ta Tsakiya daga INEC

KANO: Za’a sake zabe a akwatina 234 daga cikin kananan hukumomi 30 da aka soke -INEC

Dangalan Muhammad Aliyu

#NigeriaDecides2019: Alamu sun nuna kifewar Kwankwaso, Saraki da Dino Melaye

Dabo Online
UA-131299779-2