Zaben2019: Wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Indiya, sun bayyana murnarsu ga nasarar Buhari

A cigaba da nuna murna da farinciki da samun nasarar shugaba Muhammadu Buhari, wasu daliban Najeriya dake karatu a kasar Indiya sun bayyana irin nasu farinciki.

Tattakin da suka gudanar ranar Alhamis 28 ga watan Fabarairu 2019 a garin Jaipur, babban birnin jihar Rajasthan dake arewacin kasar ta Indiya.

Aliyu, Abbas, Yusuf, Jameel, Saleem, Bello, Shira da Abdallah
Aliyu, Abbas, Yusuf, Jameel, Saleem, Bello, Shira da Abdallah

Daliban da suka fito daga sassa daban daban na garuruwan Najeriya da suka hada da jihar Bauchi, Gombe da Kano, matasan sunce sunyi wannan tattakin domin nuna farincikinsu bisa lashe zaben 2019 da shugaba Muhammadu Buhari yayi a karo na biyu.

(Hagu): Musa Dauda. (Tsa): Yusuf Baba Mudugu. (Dama): Jamil Sa’idu Shira

Daga cikin masu tattakin su hada da Jamil Sai’d Shira, Bello Musa Kaloma, Yusuf Abubakar Kama, Jamil Babayo, Yusuf Baba Madugu, Abdullahi Saleh Muhd, Salim Rabi’u, Musa Dauda Lanzai da Aliyu Hassan Adamu.

Masu Alaƙa  Jami'an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.