Yanzu-yanzu: Sarkin Karaye ya nada Kwankwaso mukamin ‘Makaman Karaye’ kuma hakimi mai nada sarki

Karatun minti 1

Mai Martaba sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II ya daga likkafar mahaifin tsohon gwamnan kano Rabiu Kwankwaso, Majidadin Karaye kuma hakimin Madobi, Musa Sale Kwankwaso a matsayin daya daga cikin manyan hakimai masu nada sarki a masarautar Karaye dake jihar Kano.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa Sarkin na Karaye ya kuma daga likkafar hakimin Madobin daga Majidadi zuwa Makaman Karaye kana hakimi mai zabar Sarki.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ya fitar, sarkin kuma ya bayyana nan gaba kadan za’a yi bikin nadin sarauta.

Wannan na nufin hakimin na Madobi daga yanzu ya shiga cikin sahun wasu kalilan din hakimai da zasu iya zabar sarkin da zai gaji sarkin Karaye anan gaba. Kamar yadda KanoFocus ta rawaito.

Masarautar Karaye dai na daga cikin sabbin masarautar 4 da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro a ranar 8 ga Mayun 2018, wanda ya hada da ita kanta Karaye, Bichi, Rano da Gaya.

A shekarar 2000 ne dai marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya nada dattijo mai shekaru 97 yanzu, Malam Musa Sale Kwankwaso a matsayin Majidadin Kano, Hakimin Madobi, bayan kuma kirkirar sabbin masarautu 4 da Ganduje yayi, Madobi ta fada masarautar Karaye.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog