Labarai

Wasu manyan abubuwan da Buhari ya fada na saukakawa talaka a jawabinsa

Yau Lahadi 29 ga watan Maris, 2020, shugaba Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya jawabi a karo na biyu tin bayan shigowar Coronavirus zuwa Najeriya.

DABO FM ta dauko wasu daga cikin manyan abubuwan da suka hada da na saukakawa talaka da shugaban ya fada a jawabin da yayi kai tsaye misalin karfe 7 na dare.

Daga cikin manyan abubuwan da shugaban ya fada akwai;

• Shugaban ya ayyana baiwa mutanen dake rayuwa a wuraren da zasu shawala bisa hana zirga-zirga tallafin kayyakin da zasu tallafawa musu musamman wadanda suke a jihohin da aka sanya dokar hana zirga-zirga (Abuja, Lagos da Ogun)

• Kira ga ‘yan Najeriya da su rika bin shawarar da gwamnati da malaman lafiya zasu rika sanar dasu akai-akai.

• Shugaba Buhari yace dukkanin wadanda aka samu ko kuma suke dauke da cutar zasu samu cikakkiyar kula da duk abinda suke bukata.

• Rashin sanya kamfanunuwan sarrafawa da siyar da abinci a cikin dokar ta hana zirga-zirga.

• Umartar ministar ma’aikatar ayyukan agaji da kula da bala’i wajen hadin gwiwa da gwamnatin jihohi domin fito da wata hanya da zata raya tare da cigaba da gudanar da shirin gwamnatin tarayya na ciyar da makaratu domin fadada ciyarwa ga al’umma.

• Kara wa’adin watanni 3 akan wadanda zasu dawo da bashin kudaden da suka karba daga shirin TreaderMoni, MarketMoni da FarmerMoni. Kuma zasu dawo da kudin ba tare da tara ba.

• Hakazalika shugaba Buhari ya sake kara wa’adin dawo da basussukan da gwamnatin tarayya ta bayar ta hannun Bankin Noma, Bankin Masana’antu da Bankin taimakon shigowa da fitar da kayayyaki.

Karin Labarai

Masu Alaka

Halayyar Buhari ta gaskiya ta bayyana bayan darewarshi shugabancin Najeriya – Buba Galadima

Muhammad Isma’il Makama

Nuna alhinin kisan wani dan Legas da shugaba Buhari yayi ya janyo cece-kuce

Dabo Online

Alhaji Aminu Dantata ya bai wa jihar Kano Naira miliyan 300 don yakar Coronavirus

Dabo Online

Tinda China da Indiya suka cigaba, babu abinda zai hana Najeriya ci gaba – Buhari

Dabo Online

Sai na kashe Buhari – Victor Odungide

Dabo Online

Yadda ake ciki game da Koronabairas a jihar Yobe

Ibraheem El-Tafseer
UA-131299779-2