Zamu fara kama iyayen da basa saka ‘yayansu a makaranta – Malam Adamu

Gwamnatin tarayya zata fara kamen iyayen da suka ki saka ‘yayansu a makaranta.

Da yake bayyana jawabi a taron  manema labarai na ma’aikatar ilimi, Ministan Ilimin Najeriya, Malam Adamu Adamu yace nan bada jimawa ba gwamnati zata fara kama iyayen da suka ki saka yaransu a makarantu.

“Baza’a dena samun rashin saka yara a makaranta ba har sai an mayar da rashin saka yaran babban laifi ga iyayensu. Idan aka fara kama iyayen, to lallai zasu hankalta.”

[irp posts=”3590″ name=”Ginin babban dakin karatun Abuja zai lakume Naira biliyan 50 – Ministan Ilimi”]

“Har yanzu akwai wadanda addini da al’ada ke hana a saka su a makaranta.”

“Wannan shine kudurin ma’aikatar Ilimin Najeriya nan bada dadewa ba, hukuncin masu aikata hakan, zasu kare a gidan kaso.”

Malam Adamu, ya bayyana irin yadda aka kashe kudi kimamin Naira biliyan 360 daga 2009-2014 wajen gina ajujuwa, siyen litattafai dama wasu abubuwa da suka shafi harkar ilimi a Najeriya. Kudin daya ce anyi ta’annatin su, dayawa anyi amfani dasu ba ta hanyar data dace ba.

 

Madogara

%d bloggers like this: