Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Cigaban al ummata ,da kaucewa zamba da sace sace yafi muhimmanci.

Ko lokacin ,Hisham Bin Abdul Malik da sauran manyan shugabanni ,irin haka ga  makwaɗaitan masana ya faru ,amma bai hana taƙiyyai cigaban al-amuransu ba. Hatta Hajjaju , balle yanzu haka mun san hargowar da wasu keyi wajen ƙoƙarin jefa mu fitinar gaba tsakanin Musulmai, kuma Biiznillah Allah bazai bari ba.

Kowa akwai mahangarsa, wallahi ina da ƙaruwa awannan, amma Abba cigaban jama’a ne Biiznillah, wanda zargi ya dabaibaye shi na cin amana, to wanda ya jiɓince shi, tabbas Azzalimi ne.

Ya Rage mutum Musulmi ya fifita siyasar jam’iyyah ko maslahar al’ummah. Kusancin wani garemu bai hana fifita mafi chanchanta agurbi, wallah duk wanda ya janyo abinda jama’a ke cutuwa yana sani , tun a duniya Allah bazai barshi ba ,Bi ƙudratillahi.

Masu Alaƙa  Rigar 'Yanci: Dama nasan za'a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin 'yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

In mara kunya jahili, ya tsaya takara da azzalimi, wallahi na farko yafi inganci …Amana ce ,kayi nazari, kayi bincike, kayi abinda ko abarzahu baza kayi nadama ba.

Ɗan Rashawa , ba’a bashi jagorantar Bayin Allah, لعن الله اراشي والمرتشي ،، wanda ake tuhuma baa bashi jagoran ci, har sai an barrantar dashi, ko kuma ya rantse hakan bata faru ba.

Ka ƙaraji yace uffan, ko musantawa? nace ka taɓa ji ya musa? da ƙadimi littafin Allah, me shaidar yazo , haba jama’a, wasa waje yake samu, wargi ma dama yake samu, ga Nagartacce yaya zan zaɓi Sangartacce, Kautacce?.

Masoya gaskiya sun zaɓi chanchanta da nagarta amma an toge dan Ruɗu da nufin maguɗi kawai, fataken dare suka dira satar akwatin Ƙuria, wani sintir sukai masa.

Masu Alaƙa  Shawarata ga Shugaba Buhari kan yadda za'a magance tsaron Borno da Zamfara, Daga Datti Assalafiy

Allah na tare da bayinsa, managarta, Inshaa Allah, Biiznilllahi wa Kudratihi me ƙaunar Ɓarawo , zai tuba, Ɓarawon ma fatan nadama muke masa, dan wataran ya kimtsu, Allah tallafawa Kanawan Dabo da duk masoya gaskiya da gaske.

Zaku iya tuntubarmu ta “submit@dabofm.com” domin turo naka ra’ayin.