//
Wednesday, April 1

Zan kashewa karamar hukumar Dala naira miliyan 500 -Yakudima

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Danmajalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala Babangida Abdullahi Yakudima yace zai kawo aiki na Naira miliyan dari biyar a mazabar Dala.

Rahoton mu na nan Dabo FM ya jiyo Babangida Abdullahi Yakudima ya bayyana haka ne a wani shiri na gidan Rediyan Freedom.

Yace a ayyukan da danmajalisa yake yiwa al’umma ya yayi tanadi mai kyau ga al’ummar karamar hukumar ta Dala wajen horar da matasa da bayar da jari.

Bayan haka ya dauki kwararru da zasu zo da tsare tsare masu kyau wajen ganin an samarwa al’ummar ta karamar hukumar Dala mafita a harkokin yau da kullum.

Babangida Yakudima yace a kasafin kudin shekarar 2021  kuwa zai gudanar da ayyukan da suka kai Naira biliyan daya a mazabar ta Dala.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020