Labarai

Rikici ya barke a zauren majalisar Kansilolin karamar hukumar Zaria

Mu’azu Abubakar Albarkawa.

Jihar Kaduna

  • Rikicin ya barke bayan neman majalissar ta dakatar da shugaban masu rinjaye bisa samunshi da yin zagon kasa a yunkurin da sukeyi na tsige shugaban karamar hukumar.

Tun bayan da wasu daga cikin ‘yan majalisun dokokin karamar hukumar Zaria, a jihar Kaduna, sukayi yunkurin tsige shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim a kwanakin baya, lamarin da ya bar baya da kura a siyasar karamar hukumar, a Larabar nan, majalisar ta ci gaba da zamanta na lokaci zuwa lokaci da aka saba domin ci gaba da duba al’amuran da suka shafi karamar hukumar ta Zariya.

Sai dai wani abu da ya bada mamaki da ta’ajibi shi ne, yanda aka yi musayar zafafen kalamai tsakanin bangarorin ‘yan majalisar da suke hamayya da juna.

DABO FM ta tattara cewar majalissar ta dare gida biyu tin bayan yunkurin tsige shugaban karamar hukumar duk kuwa da cewa wasu daga cikin Kansilolin sun janye kudurinsu na tsige shugaban.

A zaman da suka gabatar ranar Alhamis, kansilan mazabar Dutsen Abba, Hon Abdul’aziz Sani, ya gabatar da kudiri neman majalisar ta hukunta duk wadanda suke kawo cikas da zagon kasa ga sha’anin tafiyar da majalisar, nan take kansila mai wakiltar mazabar Kwarbai A, Hon Hussaini Sale ya goyi bayan kudirin.

Daga bisani, kakakin majalisar, Hon Hashimu Bako, ya karanto wasu laifukan da ake zargin shugaban masu rinjaye na majalisar kuma kansila mai wakiltar mazabar Kufaina, Hon Akilu Abubakar ya yi, lokacin dambarwar da ta faru a majalisar a kwanakin baya.

Daga cikin laifuffukan da aka karanto sun hada da amfani da takardar da ke dauke da tambarin majalisa wurin rubuta takardar koke kuma hakan ya sabawa ka’ida.

Nan ne shugaban majalisar Hon Hashimu Bako Wadata, ya amince a dakatar da shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon Akilu Abubakar daga zaman majalisar na tsawon watanni uku.

DABO FM ta tabbatar da fara rikicin bayan kalaman Hon Isma’il Shu’aibu na mazabar Tukur-Tukur wanda ya hassula ragowar kansilolin.

Haka zalika Hon Isma’il Shu’aibu ya karanto laifuffukan da suke zargin shugaban masu rinjayen majalissar ke aikatawa ciki har da “karbar kudade” daga hannun shugaban karamar hukumar, Injiniya Aliyu Idris, tare da rashin iya gudanar da aiki. Daga nan ne ya nemi da a dakatar da shugaban masu rinjayen majalissar ba tare da bata lokaci ba.

Daga nan ne daya daga cikin ‘yan majalisar kuma kansila mai wakiltar mazabar Kwarbai B, Hon. Ibrahim Sambo, ya nemi shugaban majalisar da ya rufe majalisar bisa kalaman da yace zasu iyaiya kawo cikas ga zaman majalisar.

Rikicin ya sake barkewa bayan wasu dayawa daga cikin kansilolin basu goyi bayan gintse majalissar ba wanda wasu kuma suka goyi bayan kawo karshen zaman na ranar.

Bayan daukar tsawon lokaci ana musayar zafafen kalamai, nan take shugaban majalisar ya rufe zaman majalisar na wannan rana.

Sai dai abun da ya daurewa manema labarai kai, shi ne yadda wasu ‘yan majalisar suka yi awon gaba da sandar majalisar bayan kammala zaman.

Bayan tashi daga zaman majalisar, Dabo FM ta nemi jin ta bakin shugaban masu rinjaye na majalisar da aka dakatar, Hon Akilu Abubakar, domin jin matsayin sa aka wannan mataki.

A cewar Hon Akilu Abubakar, yace “Tin farko matakin da aka dauka na shirya zaman majalisar ma bashi a kan ka’ida, saboda doka ta bashi daman dole sai ya san abun da za’a tattauna a majalisa kafin shigowa, sai dai akawun majalisar ya gaza yin haka.” A cewar shi, daman sun jima suna zargin akawun majalisar da sanya kanshi a sha’anin siyasa, wanda kuma ya sabawa doka da ka’ida.

A don haka Hon Akilu, ya ce yana nan daram a kan kujerar sa ba gudu ba ja da baya.

Shi ma a nashi bangaren, kansila mai wakiltar mazabar Tukur-tukur, Hon Isma’il Shu’aibu, ya ce abun da ya faru a majalisar ya zama tamkar wasan yara, domin yadda aka tafiyar da majalisar a ranar ya sauka daga doron tsarin gudanarwa na kundun tsarin mulkin jihar Kaduna.

Masu Alaka

Zaria: Kansilolin da suka sanya hannun tsige shugaban karamar hukumar sun janye

Dabo Online

Masu ruwa da tsaki sun dauki aniyar dai-daita rikicin shugabancin karamar hukumar Zaria

Mu’azu A. Albarkawa

Har yanzu shugaban karamar hukumar Zaria da Kansiloli suka tsige bai sauka ba

Dabo Online
UA-131299779-2