Siyasa

2019: Adam Zango yayi hannun riga da tafiyar Buhari

Fitattacen jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya koma goyon bayan tsohon mataimaki kuma dan takarar shugabanci kasa karkashin jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Wasu majiyoyin kusa da jarumin sun bada tabbacin barrantar Adam Zango daga tafiyar shugaba Buhari.

A kwanaki baya, jarumin ya wallafa a shafinshi na Instagram yace, “Nanda awa 24 zan sauya sheka daga jami’iyyar APC zuwa PDP, amma cikin kasa da ‘yan dakiku ya goge rubtun daga shafin nashi.

Meyasa jarumin ya bar tafiyar APC?

Itace tambayar da masoya Adam Zango dama daukacin mutane zasu so sani game da lamarin.

Muni bincike don gano ainahin dalilin jarumin.

Faifayen bidiyo dayawa sunyita yawo a kafafen sada zumuta musamman na manhajar Instagram, wanda aka gano wasu daga cikin manyan yaran jarumin kamar Mustapha Naburuska, wanda ake ganin yana daya daga cikin manyan yaran jarumi, yana kokawa akan wasu jarumawan da suke kinyi musu raba dai-dai na kudaden da suke samu idan sun fita taron yakin neman zaben.

“An kawo kaso mai kauri an bayar, kusan 25(m) amma an bimu da dari dari (dubu) sai kace ‘yayan kyanwa.” – Mustapha Naburuska.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kotun karar zaben shugaban Kasa ta yi watsi da karar kalubalantar nasarar Buhari

Dabo Online

Ramadan: Buhari yayi kira da a cigaba da wanzar da zaman lafiya, soyayya tsakanin al’umma

Dabo Online

Na dora yarda ta gareku – Buhari ya fadawa sabbin Ministoci

Dabo Online

Hanan Buhari ta kammala digiri da maki mafi daraja

Muhammad Isma’il Makama

An janye karar da aka shigar don ganin kotu ta bawa Buhari damar zarcewa a karo na 3

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Najeriya sun yanke hukunci, NNPC ta huta?, Buhari yaci zabe.

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2