(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kano: Kwankwaso, Atiku zasu iya amfani da filin wasa na Sani Abacha – KNSG

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje tace Kwankwaso, Atiku da sauran ‘yayan jami’iyyar PDP zasu iya gudanar da gangamin yakin neman zabensu a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, a cikin birnin Kano.

An shirya gudanar da taron a ranar 10 ga watan Fabarairun 2019, daga bisani gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe filin wasan domin yi wasu gyare gyare da suka hada da gyaran kujeru da saka sabon allo.

Gwamnatin ta baiwa kamfanin dake gudanar da aikin umarnin tsagaitawa har zuwa sanda za’a gama gudanar da taron.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zasu koma filin wasa dake Sabon Gari domin ci gaba da harkokin wasanninta kamar yadda kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya bayyanawa manema labarai.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog