(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben2018: Kotu ta kwace nasarar Gwamnan APC, ta baiwa na PDP a jihar Osun

Karatun minti 1

Kotu ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun tin a watan Satumbar 2018 data gabata.

Gidan Talabiji na Channels TV ya rawaito cewa Kotu ta zartar da wannan hukunci a yau Juma’a 22/03/19 tin bayan da jami’iyyar PDP ta shigar da kara gabanta, akan zaben zagaye na biyu da aka gudanar a watan Satumbar 2018.

Sanata Adeleke ya shigar da kara bisa zargin jami’iyyar APC da hukumar zabe wajen taimakawa wajen gudanar da gurbataccen zaben zagaye na biyun.

Jami’iyyar APC tace hujjojin da PDP ta bayar basu da tushe hasali ma ta shirya wasu ne da kanta.

Sai dai mai shari’a, Justice Obiora Obi ya karbi dukkanin hujjojin da PDP ta bayar, kotu ta amince zatayi aiki da su.

Bayan dan bincike da aka gudanar, kotun ta gano cewa baturen zaben jihar ta Osun a lokacin gudanar da zaben, shine ya soke akwatinan zabe 7. Wanda Kotun ta kira da bashida hurumin soke wani zabe.

Kotun ta kuma ragewa jami’un kuri’u APC kuri’u 2,029, PDP 1,246 bisa rashin yadda da kuri’un.

Daga karshe, Kotun ta yanke hukuncin soke nasarar da dan takarar jami’iyyar APC, Mr Oyetola yayi, inda kuma ta tabbatar da Sanata Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Madogara

Karin Labarai

Sabbi daga Blog