Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin gwamna Mallam Nasiru El-Rufai tace zata daukaka kara akan hukuncin da wata kotu tayi domin barin Al Zakzaky ya tafi neman magani kasar Indiya.
Daraktan kula bangaren shari’a na jihar, Mr Dari Bayero ne ya sanar da haka a ranar Talata.
A ranar 5 ga Agusta ne dai wata babbar kotu a jihar Kaduna ta baiwa shugaban haramtacciyar kungiyar IMN izinin fita kasar Indiya neman magani kamar yacce suka bukata ta hannun lauyansu, Mista Femi Falana.
Mista Dari Bayero ya bayyana cewa a ranar Laraba, gwamnatin jihar zata daukaka kara akan hukunci kotu tare da kalubalantar wadansu daga cikin sharudan da kotu ta gindayawa Sheikh Zakzaky a yayin tafiyar tashi zuwa Indiya.
