Home LabaraiKotu ta kwace zaben ‘Yan Majalissun jiha guda 2 daga APC ta baiwa PDP a jihar Adamawa

Kotu ta kwace zaben ‘Yan Majalissun jiha guda 2 daga APC ta baiwa PDP a jihar Adamawa

by Dabo Online
0 comments

Kotun dake sauraren korafin zaben Majalissar Dokoki dake da zama a jihar Adamawa, ta kwace zaben ‘yan majalissun jiha na jami’iyyar APC guda 2.

‘Yan Majalissun su hada da Hon Shu’aibu Langa, mai wakiltar shiyyar Mubi ta Arewa da kuma Hon. Musa Ahmad Bororo.

Kotun ta soke zaben Hon Shuaibu Langa ne bisa dalilin mikawa hukumar INEC takardun bogi wanda suka nuna ya kammala karatun Firamare.

Tini dai kotu ta baiwa INEC umarnin baiwa dan takarar PDP, Suleiman Vokna, takardar shaidar lashe zabe.

Haka zalika, kotu ta kwace zaben Hon Musa Ahmad Bororo, bisa dalilin amfani da sunaye daban daban har kala uku a cikin takardun daya aikewa hukumar zabe ta INEC.

Kotun dai ta baiwa hukumar zaben umarnin baiwa dan takarar PDP, Musa Dirbishi, takardar lashe zabe.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00