Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Mallam Haruna Muhammad Sani Ibn Sina, ta bayyana cewa dokar hana cakudar Mata da Maza a baburan adaidata sahu tana nan daram.
Shugaban ya bayyana haka yayin da yake ganawa a cikin shirin Guziri mafi alheri na gidan rediyon Arewa dake Kano.