Home SharhiSharhi: Wasu daga cikin farfagadar mabiya ‘Kwankwasiyya’ da suka yadu

Sharhi: Wasu daga cikin farfagadar mabiya ‘Kwankwasiyya’ da suka yadu

by Dabo Online
0 comments

Biyo bayan takaddama data afku a wannan mako da muke fita daga ciki na kama wani matashi dan darikar Kwankwasiyya da hukumar tsaro ta farin Kaya a Najeriya ‘DSS’ tayi, matashin da aka tabbatar da kasancewarshi wanda ya hada bidiyon gayyatar mutane zuwa daurin auren da ba gaskiya bane na shugaba Buhari da Minista Sadiya Faruk.

DABO FM tayi duba cikin ra’ayoyin mutane da kuma dan bincike da muka gudanar bisa ga irin zantuttukan da mabiya tsagin jar hula suka rika yadawa a baya, wanda kuma bincike ya tabbatar da basu da tushe.

Karfi da tasiri darikar jar hula a kafafen sadarwa yasa kusan duk abinda ya fito daga ‘ya’’yan gidan, nan da nan yake faruwa.

Ga wasu daga jerin zantukan mabiya tsagin wadanda bincike ya tabbatar da basu faru ba.

  1. Gabannin fara shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, mabiya tsagin jar hula sun ce; Barista Bulama Bukarti, yace zai kawo lauyoyi 100 wadanda zasu kalubalanci nasarar gwamna Ganduje a kotun zabe.

A ranar 28 ga watan Maris din 2018, Barista Bulama Bukarti yace; “Banida Masaniya akan Lauyoyi 100 da akace zan jagoranta domin kare Abba K Yusuf a Kotu

2. Kwana daya kafin sake zaben zagaye na biyu na zaben gwamnan Kano, mabiya tsayin sunyi ta yada cewar; Asiwaju Bola Tinubu yazo Kano don murde zabe.”

A ranar 20 ga watan Maris, Bola Tinubu ya fito ya tabbatar da cewar baizo Kano ba. (Tushen Jaridar The Nation da Punch)

Mu hadu a kashi na biyu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00