1
Rundunar Sojin Najeriya tace ta samu nasarar dakatar da wani hari da kungiyar Boko Haram tayi yunkurin kai wa a garin Damaturu na jihar Yobe.
Tin da yammacin Lahadi, wasu mazauna yankin suka shaidawa DABO FM jin karar harbe-harbe wanda ta kai ga wasu sun kauracewa yankin.
Kakkakin sashen ‘Operation Lafiya Dole’, Laftanar Chinonso Oteh ne ya tabbatar da fatattakin da jami’an suka yi wa Boko Haram a harin da sukayi yunkurin kaiwa zuwa garin.
Tini dai aka cigaba da gudanar da rayuwa a garin dake kusa da babban titin Gashua a garin Damaturu.
