A jihar Imo, an kwantar da wani babban likita mai sunan Cherechi Okonko a sashin bayar da agajin gaggawa na gwamnatin tarayyar Najeriya dake garin Owerri sakamakon raunuka da mai dakinshi tayi masa.
Kamar yadda PUNCH ta bayyana, matar likitan a matsayin ungozoma ta cire wa mijinta nata hakwaran saman baki tare da cire masa iyakar harshe dake iya fitowa daga baki da wani sashen ganda.
PUNCH ta tattara cewar tini dai aka garzaya da likitan zuwa asibiti yayin da yake a yanayin da bai san inda kanshi yake ba.
Mijin ungozomar ya kasance a likitan sha’anin Mata dake aiki cibiyar lafiya ta tarayya dake Owerri.
Wani ma’aikacin a asibitin da ya bukaci a boye sunanshi ya bayyana cewar; “Uwarigidan wani wani likitan cibiyar kiwon lafiya ta ji masa rauni mai muni bayan sa-in-sa tsakaninshi da matarshi.
Yace; “matar ta yanke masa hanci, hakwaranshi na sama, gaban harshenshi da wani sashe na ganda a cikin bakinshi. Ta kuma kira mahaifiyarshi tace tazo ta dauki gawar ‘danta.
“Likitan ya taki sa’a, an garzaya da shi zuwa asibiti da gaggawa a cikin dare inda aka samu kanshi. Duk da ya samu kanshi, har kawo yanzu baya iya magana.
Kakkain yan sandan jihar ya bayyana har yanzu labarin bai iske rundunar ba.
