Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 5 da safiyar yau Litinin.
KAmar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 35.
Da safiyar yau da misalin karfe 9:45, an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 5. 2 a jihar Legas, 2 a Abuja da guda 1 a jihar Edo wanda ya hada jimillar wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 35.”
Five new cases of #COVID19 have been confirmed in Nigeria: 2 in FCT, 2 in Lagos & 1 in Edo