Home LabaraiJihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

by Aisha Muhammad
0 comments

Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta na shiga jihar domin rigakafin kamuwa da cutar Coronavirus.

Gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ne ya bayyana haka yayin wani taro da ya kira a daren yau Alhamis a fadar gwamnatin jihar dake garin Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnan yace gwamnatin ta yanke shawarar rufe iyakokin jihar ne bayan gama tattaunawa da karbar shawarwarin ma’aikatan lafiya da hukumomin tsaro.

”A wannan dare, mun tsaya tare da jami’an tsaro domin mu sanar daku matakin da muka dauka na tabbatar da cewar mun tsare al’ummar wannan jiha daga kamuwa da wannan cuta da ta addabi duniya.”

“Munyi shawara da sauran gwamnonin Najeriya cewar yau zamuyi bayanin rufe jihohinmu.”

“Mun rufe jihohinmu ba fita, ba shiga. Babu motar da zata shigo jihar Zamfara, babu motar da zata fita.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00