Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 51 a daren Juma’a .
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 493.
“A yau da misalin karfe 10:10 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 51. An samu guda 32 a Lagos, 6 a Kano, 5 a Kwara, 2 a Abuja, Oyo da Katsina sai guda 1 a jihohin Ogun da Ekiti.”
Fifty-one new cases of #COVID19 have been reported;
32 in Lagos 6 in Kano 5 in Kwara 2 in FCT 2 in Oyo 2 in Katsina 1 in Ogun 1 in Ekiti
As at 10:10 pm 17th April there are 493 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria.