1
Allah Ya yi wa Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim rasuwa yau a jihar Kano.
Hakan na zuwa cikin kasa da sa’o’i 24 da rasuwar mai martaba Sarkin Rano, Alhaji Abubakar Tafida Ila.
Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim Makama ne ya sanar da haka yau Lahadi.
Kafin rasuwarshi ya kasance Jarman Kano, mukamin da ya samu tin bayan mutuwar marigari Alhaji Muhammadu Dan Kabo.
Haka zalika ya kasance tsohon malami a Jami’ar Bayero dake jihar Kano.
