0
Sarkin Kaura Namodi a jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Asha, ya rasu a yau Lahadi.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kasa da 24 bayan rasuwar Sarkin Rano a jihar Kano, Alhaji Abubakar Tafida Ila da kuma sa’o’i kadan bayan mutuwar Jarman Kano, Farfesha Isa Hashim.
Sarkin Kaura Namodi ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya kamar yadda ‘dan uwanshi, Abdulkarim Muhammad ya bayyana.
Ya kara da cewa mamacin ya sha fama da ciwon sikari da hawan jini.
Ya ras yana da shekaru 71.
