1
A ranar Juma’a fitattacen jarumin Adamu Zango ya tasa keyarshi zuwa jami’iyyar PDP bayan wata ‘yar takadda da abokan sana’arshi a Kannywood.
A shirye-shiryen gudanar da taron Kamfen din Atiku a Kano, jarumin ya karbar darikar Kwankwasiyya a yau daga hannun Madugun darikar Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma dan takarar gwamna a jami’iyyar ta PDP, Engr Abba Kabir Yusuf.
Ana sa ron karbar jarumin a filin taron tare da magoya bayanshi sama da mutum dubu hamsin.
