Gwamnati jihar Bayelsa ta baiwa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan babban mai bada shawara a Asusun Cibiyar Habbaka Ilimi ta jihar Bayelsa.
Gwamnan jihar Seriake Dickson ne ya bayyana haka a wajen bude cibiyar a garin Yenagoa, babban birnin jihar.
Gwamna yace tsohon shugaban kasar shine zai rike cibiyar tare da sa ido akan yadda ake tattara kudin asusun cibiyar.
Dickson ya kara da cewa; Goodluck Jonathan ne kashin bayan cigiban Ilimin jihar Bayelsa bisa hubbasar da yayiwa bangaren lokacin da yake gwamnan jihar Bayelsa.
Majiyoyin DaboFM da Jaridar Daily Trust sun tabbatar cewa; Dr Goodluck Jonathan ya karbi aiki tare da alkawarin yin bakin kokarinshi wajen ciyar da Ilimi dama asusun jihar gaba.
