(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Abdullahi Shehu ya biyawa Marayu 130 ‘yan jihar Sokoto kudin Makaranta

Karatun minti 1

Shahararren dan kwallon Nijeriya, dan asalin jihar Sokoto, mai taka leda a kungiyar Busaspor dake kasar Yurkiya, Abdullahi A Shehu ya dauki nauyin yara marayu da marasa gata kudin karatun gaba da sakandire a jihar Sokoto.

Ya biyawa matasa ‘yan asalin Sokoto kudin karatu a makarantu daban-daban a fadin jihar ta Sokoto.

Wanda kudin sun kai kimanin naira milyan daya, (1,000,000) a makarantu daban daban a fadin wannan jiha.

Abdullahi Shehu ya biya kudadden ne karkashin gidauniyar da ya kafa domin taimakawa talakawa, wato Abdullahi Shehu Foundation wadda Ahmad Tijjani ke jagoranta.

Gerin Makarantu da adadin daliban daya biyawa:

Shagari College of Education Sakkwatto, ya biyawa mutun 40.

State Polytechnic sokoto ya biyawa mutum 40

Haka ya dauki nauyin biyawa mutum hamsin 50 kudi domin gyara takardun karatunsu a matakin sakandare domin su samu cigaba da karatunsu a mataki na gaba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog