(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben2019: Siyar da NNPC dole ne a wajena – Atiku

Karatun minti 1

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace yana nan akan matsayinshi na siyarda ma’aikatar NNPC.

Atiku ya bayyana haka ne yau, a wani taro daya halartar na ‘yayan jami’iyyar a jihar Kaduna.

Saidai a wannan karan yace bazai siyarwa da abokananshi ba.

Yace kamfanin ya gaza gudanar da aikin da aka kafa kamfanin donshi, shiyasa yaga dacewar siyarda da kamfanin.

“Siyarda kamfanin NITEL shine yau ya bamu damar yawaitar wayar hannu cikin sauki, shiyasa naga ya dace a siyar da NNPC.”

Ya kara da cewa, gwamnatin shi zata baiwar ilimi muhimmanci ta hanyar bada tallafin karatu da ingantanta makarantun cikin kasa.

Yayi alkawarin baiwa matasa kaso 30 cikin dari a mukaman gwamnatinshi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog