//
Sunday, April 5

Alkaluman ‘Corona Virus’ ya zama 35 bayan sake tabbatar da 5 a safiyar Litinin

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 5 da safiyar yau Litinin.

KAmar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 35.

Da safiyar yau da misalin karfe 9:45, an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 5. 2 a jihar Legas, 2 a Abuja da guda 1 a jihar Edo wanda ya hada jimillar wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 35.”

Masu Alaƙa  Gwamnatin Kano ta musanta shigar da Corona Virus cikin jihar ta filin Jirgi

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020