/

Aminu Ado Bayero ya tsige jigo a jihadin Shehu Bn Fodio wanda ya nada marigayi Ado Bayero sarki

dakikun karantawa

Biyo bayan sanarwa da ta gabata daga Masarautar Bichi ta jihar Kano bisa tsige wasu hakimai guda 5 (dake karkashin Masarautar kamar yacce sabuwar dokar Sarakunan jihar ta tanada) bisa rashin yi wa Sarkin Bichi mubaya’a.

Daga cikin hakiman akwai Sarkin Bai – Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtar Adnan (Shugaban Kabilar Dambazawa) wanda akanshi DABO FM za tayi duba cikin tarihi na kafuwar daular Usmaniyya ta jihar Kano.

Muhimman abubuwa game da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan;

  • Sakataren Majaliisar masu nadin Sarakunan Kano.
  • Kwishinan Ilimi na farko a jihar Kano.
  • Tsohon dan Majalissar kuma tsohon bulaliyar Majalissart tarayyar Najeriya.
  • Sunanshi ne sanye a makarantar Sakandire ta Day Science College Kano.

Alhaji Mukhtar Adnan ya zama dan majalissar mai nadin Sarkin Kano a shekarar 1954 inda bayan shekaru 9 suka nada Marigayi Dr Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a 1963.

Sarkin Bai, shine shugaban kabilar Dambazawa, wadanda tarihi ya nuna sun taimakawa Shehu Usmanu wajen yakunan jihadin da aka dauki shekaru ana fafatawa.

Dambazawa sun taimaka wa Shehu Bn Fodio ta hanyar samar da dakarun yaki a garin Dambatta tare da yin tsare tsaren yakin.

Bayan da Shehu Dan Fodio ya ci garin Kano da yaki, an shafe shekaru 3 daga shekarar 1806 zuwa 1807 babu Sarki a jihar Kano inda jagororin jihadi guda 5 suke rike da mulkin Kano.

Jagororin sun fito daga kabilun Sullubawa (Mallam Jamo), Yolawa (Mallam Jibir), Jobawa (Mallam Bakatsine) , Hausa (Mallam Usman Bahaushe) da Dambazawa (Mallam Muhammadu Yunusa Dabon Dambazau – Wanda muke magana a kanshi.

Kasancewar goyon baya da taimakon da wadannan kabilu sukayi wajen yin jihadin Shehu Usmanu yasa suka kasance masu nadin Sarki wanda daga bisani har ta kai ga Mallam Dabo na kabilar Dambazawa da sauran kabilun Fulani suka ki goyon bayan Sarki Sulaimanu da Shehu ya nada. Har ta kai ga Sarki Sulaimanu ya tsare Dabon Dambazau a kurkuru kafin daga bisani har ta kaisu gaban Shehu suka samu sasanci a tsakani.

Dalilin da yasa taba Sarkin Bai ya zama taba Shehu Usmanu

Kasancewar mutanen kabilar Dambazawa (Inda Sarkin bai ya fito) Fulani ne, jagoransu a wannan lokaci da na sauran kabilun Fulani suka je wajen Shehu domin yin karatu a wajenshi wanda har yakin da Shehu yayi a Gudu ya riske su.

Bayan dawowar shugaban Kabilar Dambazawa, Modibbo Muhammad Yunusa (Dabon Dambazau) ya hada kan mutane domin bin shugabancin Shehu Usmanu (Tin asalinsu dama Musulmai ne).

Wanda suka zama manyan jigogin yaki da Shehu Usmanu yayi da Kano wanda har ya samu nasarar cinye garin Kano.

Bayan yaki da shekara 3, Shehu Usman bai nada sarkin Kano ba sai dai jagororin Fulanin Kano guda biyar wanda daga ciki har da Sarkin Bai (Dabon Dambazau) ne suke rike da madafun ikon Kano.

Sultan Muhammadu Bello magajin Shehu kuma da ga Shehu Usmanu, shi ne da kanshi ya bawa Dabon Dambazau sunan Sarkin Bai bayan da Sarki Sulaimanu ya rasu a wajen da aka nada Sarki Ibrahim Dabo.

A wata mujallar tarihi mai taken “The Fulani Emire of Sokoto” ta tabbatar da mubaya’ar kabilar Dambazawa ga Shehu Dan Fodio tin kafin ya yaki Sarkin Gobir a shekarar 1802 zuwa 1808.

Kasancewar Kabilar Dambazawa a garin Dambatta suke yasa su ke rike da Hakimcin garin Dambatta da Makoda kuma ake wa sarautar lakabi da Sarkin Bai (Sakamakon gidan da suka fara bayan karbe garin Kano da Shehu Usmanu yayi – Gidan Bai, unguwar Dambazawa, Kasuwar Jakara.).

Kabilar Dambazawa sun kasance masu yawo daga gari zuwa gari suyi yado har ma duk inda suka zauna suke kiranshi da Dambazau, wanda a yau akwai shi a garuruwan Bauchi, Kano, Katsina, Sokoto da Taraba.

Karanta cikakken tarihin anan;

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog