An bukaci ‘Yan Kano su zauna lafiya bayan kammala yanke hukuncin shari’ar Abba da Ganduje

Dabo FM, tana kira ga al’ummar jihar Kano, su zama masu da’a da kuma masu kawowa jiharsu zaman lafiya a yayin yanke hukuncin kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamnan jihar.

Ana kallon shari’ar tsakanin gwamnan Kano, Dr Ganduje da kuma dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wacce tafi kowacce jan hankali a duk shari’ar da aka gabatar.

Kotun dake sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, ta bayyana ranar da zata kawo karshen karshen Shari’ar da aka kalubalanci nasarar gwamnan Kano, Dr Ganduje.

Kotun da mai shari’a Halima Shamaki, take jagoranta ta ayyana ranar 2 ga watan Oktobar 2019 a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Dan takarar jami’iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf ne dai ya shigar da karar inda yake kalubalantar bayyana Dr Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben.

Masu Alaƙa  Kotu ta soke zaben dan Majalissar APC a jihar Kano

A watan Satumba, dukkanin bangarorin 3, APC, INEC da PDP sun gama bayyanawa kotu dukkanin hujjoji da kariyarsu, inda daga nan Kotu tace zata sanya ranar da zata yanke hukuncin.

Tin da dari dai PDP tace dan takararta ne ya samu nasara a zaben farko wanda aka gudanar a watan 9 ga watan Maris, 2019.

Sai dai a bangaren APC da INEC, sun bukaci kotu tayi watsi da karar bisa rashin ingantattun hujjoji da PDP ta gabatar.

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.