Labarai

Sheikh Bala Lau ya ziyarci filin masallacin da aka rusa a Fatakwal dake Jahar Ribas

Shugaban kungiyar Izala Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau da tawagarsa, ya ziyarci filin da gwamnatin jihar Rivers ta rusa Masallaci inda dubannin Al’ummar musulmi ke gudanar da salloli biyar tare da sallar juma’a a wajen.

Dabo FM ta samu rahoton ne cikin wata wallafa a shafin kungiyar Izala na yanar gizo a ranar talata 1 ga oktoba, inda shafin ya kara da cewa, Sheikh Bala Lau ya nuna matukar kaduwa da yaga lamarin a zahiri, ya kuma kira al’ummar musulmi mazauna Portharcort da su zama masu bin doka da oda, su jira har zuwa lokacin da shugabanni zasu tuntube su.

Shugaban Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Rivers da tayi gaggawan bada daman Gina wannan masallaci da kuma sulhuntawa da Al ummar musulmi na jihar dama kasa baki daya

A karshe Shehin Malamin ya karfafa musu gwuiwa kan Allah da kansa zai kare addinin sa daga makiya da azzalumai, dan haka wannan ba sabon Abu Bane a cikin addinin musulunci. Kuma musulunci shi ke da Nasara insha Allah.

Tawagar da ta rufawa shehin Malamin baya ta hada da; Sheikh (Dr) Kabiru Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, Engr. Mustapha Imam Sitti, Sheikh Aliyu Burga Azare, Sheikh Ibrahim kasuwar Bacci, Alaramma Ahmad Suleiman, Alaramma Nasiru Gwandu, da dai sauran su.

Masu Alaka

Kungiyar Izala ta kai ziyarar jaje ga Sambo Dasuki kwanaki 3 bayan sakinshi akan zargin “Sata”

Dabo Online

Tarihi: Sarkin Musulmai Sir Abukabar III ne ya rada wa kungiyar IZALA suna

Dabo Online

Neman Taimako: Kujerar gwamnan da ka hau ta gidanku ce? – Sheikh Jingir ga Masari

Dabo Online

‘Yan Sanda sun samu nasarar bundige Iblis a Najeriya

Daukar lauyan da ba Musulmi ba ya jawo wa IZALA cece-kuce

Dabo Online

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2