Labarai

An sace fiye da mutane 60 a Kaduna, mutum 6000 na kan hanyar gudun hijira a jihar

Dubban mutane na tserewa daga kauyuka daban-daban na yankunan kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari inda suke neman mafaka a garin Buruku na jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

BBC ta rawaito, yankin dai na Birnin Gwari ya jima yana fama da rikice-rikice musamman na barayin shanu da ‘yan bindiga dadi da kuma masu garkuwa da mutane.

A hare-haren da ‘yan bindiga ke kai musu a ‘yan kwanakin nan, al’amarin ya yi sandin asarar rayuka da raunata mutane da dama, baya ga awon gaba da ake zargin maharan sun yi da mutane da kayayyaki.

Rahoton Dabo FM cikin wani faifan bidiyo na tattaunawar BBC da wani mutumin yankin wanda bai so a ambaci sunansa, ya shaida cewa kauyukan da wannan lamarin ya shafa sun hada da Rimana da Malmo da Ba’da da Zankoro da Ba-dole da Ba-dumi da kuma Sarari.

A yanzu haka dai da dama daga cikin ‘yan kauyukan na karamar hukumar Buruku ta jihar Kaduna inda a can ne suka samu mafaka.

Wani daga cikin masu gudun hijirar ya shaida cewa akalla za su kai su 6,000 a garin na Buruku. Masu gudun hijirar dai sun kunshi maza da mata da yara kanana.
Sun kuma shaida cewa ba su samu taimako daga wurin hukumomi ba ta fuskokin abinci ko magunguna ko kuma muhalli.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani kan wannan lamarin inda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na da labarin abubuwan da ke faruwa kuma tana kokarin shawo kansu.

Matsalolin tsaro musamman na ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane na kara kazanta a jihohin arewa maso yammacin kasar musamman Katsina da Kaduna da jihar Zamfara.

Inda kuma yankin arewa maso gabashin kasar musamman jihar Borno ‘yan kungiyar Boko Haram da Kuma ISWAP ne ke cin karensu ba babbaka.

Karin Labarai

Masu Alaka

Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya – APC

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin Kaduna ta shirya yiwa Dawakai 1000 allular rigakafin kamuwa daga Zazzabin Dabbobi

Dabo Online

Masu Garkuwa sun kashe ‘yar shekara 8 tare da jefa gawarta cikin Rijiya a Kano

Dabo Online

EFCC ta damke wani Kansila a Kaduna da laifin lamushe naira Miliyan 11

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisa a Jigawa

Muhammad Isma’il Makama

Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta amince a bude shagunan kayyakin abinci da na magani

Dabo Online
UA-131299779-2