//
Thursday, April 2

EFCC ta daskarar da asusun bankin Shehu Sani, an bukaci a gayyato Samaila Isa Funtua

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC ta daskarar da asusun bankin tsohon sanatan Kaduna, Sanata Shehu Sani.

Dabo FM ta ruwaito sanarwar ta fito ta bakin mai bawa tsohon sanatan shawara, Suleiman Ahmed, a safiyar Lahadi, inda ya kara da cewa hukumar ta kuma tilastawa sanatan bayyana kadarorin sa.

Suleiman dai ya zargi hukumar da wariya wajen binciken da take, inda ya ce menene dalilin da bata gayyaci wanda ya kai karar ba.

Haka kuma cikin abin da ya kira da kazafi, yace tilas a gayyato babban na hannun daman shugaban kasa, Samaila Isa Funtua saboda bayyanar sunan sa cikin takardar dake kunshe da zargin tsohon sanata Shehu Sani.

Masu Alaƙa  Mai maganin gargajiya ya damfari wani dan Koriya ta Kudu miliyan 30 akan zai nemo masa lasisin NNPC

Tini dai Shehu Sani ya karyata zargin da ake masa na karbar na goro kimanin $25,000 a hannun wani shugaban kamfanin saida motoci na ASD Motors, Sani Dauda domin a bawa shugaban EFCC, Ibrahim Magu kan rufa rufar wani bincike daya shafi Dauda Sani. Kamar yadda TheCable ta wallafa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020