//
Thursday, April 2

Ba ƙaramin namijin ƙoƙari nake wajen mulkar Najeriya ba tare da ta wargaje ba -Buhari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban Kasar Najeriya, Muhammad Buhari ya bayyana cewa yana mulkin Najeriya ne cikin nutsuwa da kokarin tabbatar da hadin kan kasar.

Bayanin yana kunshe cikin wata takarda da mai bawa shugaban kasa shawara, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, kamar yadda rahoton mu na Dabo FM ya bayyana.

A yayin da yake bayanan biyo bayan takardar da jakadan amurka, Ms. Mary Beth Leonard ya aike wa gidan gwamnatin Najeriya.

Buhari yace “Ina mulkin Najeriya ne cikin nitsuwa da lissafi. Ba karamin kokari bane yin mulkin Najeriya ba tare da kasar ta wargaje ba.” Kamar yadda jaridar RippleNigeria ta ruwaito.

Takardar dai tayi martani ne game da kiraye kirayen da hukumomin kasashen waje gami da amurka na gwamnati ta dena take hakkin bil’adama.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020