Zamfara: Kotun ‘Allah Ya Isa’ ta kwace zabe daga APC da bawa PDP

Babbar kotun kolin Najeriya, ‘Supreme Court’, ta ruguje zaben cikin gida na jami’iyyar APC, ta kuma ayyana jami’iyyar PDP a matsayin jami’iyyar data lashe zaben gwamnan jihar tare da dukkanin ‘yan takarkarun jami’iyyun da suka zo na biyu a babban zaben da aka kammala a jihar.

Babban mai shari’a na kasa, CJN Tanko Muhammad, ne ya jagoranci shari’ar, tare da bayar da umarnin watsi da dukkanin wadanda aka ayyana sun lashe zabe a jihar, wadanda suke a karkashin jami’iyyar APC.

Mai Shari’a Paul Galinje, wanda ya karanto hukunci yace, Kotun ta gamsu da hukunci da wata kotun jihar Sokoto ta fitar na cewa, jami’iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba kuma jami’iyyar ba tada wani dan takara da zai shiga zaben 2019, kamar yadda majiyoyin DaboFM suka bayyana.

Ya bayyana cewa dukkanin kuri’un da APC ta samu sun tashi a iska, tare da tabbatar da cewa, kuri’un sauran ‘yan takarkaru da jami’iyyunsu, sune halastattu.

DaboFM ta tattabatar da hukuncin ya hada da gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, wanda ya tsaya takarar Sanata karkashin jami’iyyar ta APC.%d bloggers like this: