Yanzu-yanzu: INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewa ta soke jam’iyyu kimanin 74 a Najeriya, inda ta mayar da jam’iyyun siyasar zuwa 18 daga 92.

Majiyar Dabo FM ta rawaito cewa Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.

Farfesa Mahmaud ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakin ne bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta na yiwa jam’iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam’iyyu. Kamar yadda BBC ta fitar.

Masu Alaƙa  An saukar min da wahayi zanyi shugabancin Najeriya -Yariman Bakura

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.