Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Budaddiyar wasika ga Dr Rabiu Kwankwaso, Daga Comr. Muzakkir Rabi’u

5 min read

Assalamu Alaikum,
Tareda Girmamawa nake Rubuta maka wannan budaddiyar Wasika a gare ka domin tunasar dakai wasu muhimman batutuwa na Siyasa daka manta dasu.

A ‘Yan kwanakin Nan najika Kanata magana akan Butulci, Butulaye da anyi maka Butulci. Madugu zanso na Tunatar dakai yadda Siyasar ka ta kasance tun a Jam’iyyar SDP Tsakanin 1991 – 1993 sanda kaje Majalisar wakilai Zuwa yau da kake Kokarin kafa Sirikin ka Kuma Karen Farautar ka a matsayin Gwamnan Kano duk da naji Wata Babbar Kotu ta Rushe Dan Takarar Naka.

Nasan bazaka manta da yadda Marigayi Alh. Abubakar Rimi da Dattijo Dauda Dangalan ya Jagoranci Jam’iyyar SDP sanda kaje Majalisar wakilai da Adalci ba tareda mugunta ko kyashi ba, ba Kamar yadda naji Su Rogo da sauran Yan Takara sunata kokawa ba a halin yanzu. Shi Din dai Dr. Abubakar Rimi Tareda Mai Girma Ambassada Aminu Wali da Alh Musa Gwadabe Sune Murhun da Suka Jagoranci Farfado da Siyasar ka a DPN da Kuma PDP a shekarar 1998 – 1999 Amma meya biyo baya tsakanin ka dasu Daya bayan Daya Sanda ka Zama Gwamna a 1999 – 2003?
Nasan Wannan ma sunan sa Butulci.

Nasan kasan Cewar Ka samu Nasara ne a daidai Lokacin da Ganduje ya futa daga ANC gidan Amb. Aminu Wali, Sannan aka Soke Takarar Malam Abba Dabo daga ANC Gidan Ambassada Aminu Wali, Inda akayi Hadin Guiwa Tsakanin ANC ta Ambassada Aminu Wali da PDM ta Alhaji Musa Gwadabe inda ka futo ka samu Nasara a Wancan Lokaci ne ka zabi Sanata Bello Hayatu a matsayin Mataimakin ka, Jagorori suka Zabi Abdullahi Umar Ganduje Wanda yazo daga tsagin ‘Yan Santsi Domin Samun Daidaito.
Amma daga baya babu irin cin Mutuncin da baka yiwa Alh. Abubakar Rimi ba, Shi kuwa Alh Musa Gwadabe Sakawa kayi aka cire shi daga mukamin sa na Minista Wanda Shima Babban Butulci ne, ba’a Maganar Sanata Hamisu Musa Domin Shima ya karbi Sakamakon Futo dakai da Yayi daga Siyasar Madobi a matakai daban daban, Mai Girma Ambassada Aminu Wali Shine Kadai ya tsira Saboda ya fika Kima da Mutunci a wajen Gwamnatin Tarayya ta Wancan Lokaci.

Daya daga cikin dalilan faduwar ka zabe a 2003 harda Wancan Butulci daka yiwa Manyan Jagorin ka da Kama karya da ciwa Manyan Mutane Mutunci, Domin Na tuna Lokacin da Marigayi Alh Abubakar Rimi Yake Mana Lacca a Gidan Akida Yake Cewa: “Anci Mana Mutunci Amma Zamu Huda lema a tsakiyar Damuna Kwankwason Uwar Kowa ya jike”.

A 2007 Akalla Mabiyan ka sama mutum 7 Sun same ka sun naimi goyon bayan ka akan zasu yi Takarar Gwamna Kuma ka Amince musu, (Cikin su Harda Ganduje, Imam Salisu Buhari, Aminu Dabo, Yusuf Kibiya da Sauransu) Amma daga bisani Sai kace kaima kanada bukata duk da kasan kanada white paper wadda Gwamnatin Shekarau tayi maka Saboda wasu laifuka daka aikata akan wasu makudan kudade Lokacin da ludayin ka ke kan dawo, Haka kazo ka murkushe su daga baya ka kawo Ahmad Garba Bichi Wanda ya Gaza Kai banten sa Saboda Wancan Butulci da Zalinci da kayiwa mabiyanka Yan Takara.
A 2011 Kuwa, Kowa yasan Yadda Ambassada Aminu Wali, Shugaban Kasa Good luck Jonathan da sauran Jagorori Suka yi tsayin daka Saika dawo Amma a 2014 Ka rikide ka fice daga Jam’iyyar ta PDP ka Zama Babban Dan Adawa dasu, Amma Kai a Wurin ka bakai Butulci ba.

Abinda yafi daukar hankalin Kowa shine yadda ta Kasance tsakanin ka da Yan Kungiyar ka ta Kwankwasiyya da Halifan ka Dr. Ganduje.
A 2015 anyi taron dangi an kafa Gwamnatin Ganduje ka bada kaso mafi tsoka Cikin Masu rike da Mukamai Amma abin takaicin ka hanasu su zauna Lafiya da Mai Girma Gwamna Wanda hakan Yayi Sanadiyyar ficewar Manyan mukarraban ka irinsu Sakataren Gwamnati Rabiu Sulaiman Bichi, Mataimakin Gwamna Prof. Hafiz Abubakar, Kwamishina Faruk Bibi Faruk Cikin wasu da dama.

Zaka iya Tunawa Dr. Dangwani yabi ka, Yayi Biyayya Tsahon Shekaru har yasha dauri a sanadiyyar ka, Rabiu Sulaiman Bichi ya hakura da mukamin sa har da Shan Kokara aka a taron hawan daushe duk a dalilin ka, Prof Hafiz Abubakar ya ajiye Kujerar Mataimakin Gwamna a dalilin ka, Aminu Dabo ya Kashe makudan kudaden sa a dalilin ka Amma da kazo tsayar da Dan Takarar Gwamna saika juya musu baya ka dauko Sirikin ka Kuma Karen Farautar ka a Kokarin da kake na cigaba da mulkar Kano a Karo na uku. Zanso Ka Fahimtar Dani ko Wannan ma Butulci ne?

Idan zakai wa kanka Adalci zaka daina magana akan Butulci a kowanne Mataki, Domin Nasan zaka yarda Dani a Kano ba’a taba yin wani Dan Siyasa daya yiwa wadanda Suka taimake shi Butulci Kamar ka ba.

Irin wannan Halin Naka shi yaja maka shiga Halin da kake Ciki, a yanzu dai Atiku ya dawo daga Rakiyar ka Saboda Zalintar sa da kayi na rike kudaden sa, bayaga kayar da ‘Yan Takarkaru na Sanatoci da ‘Yan Majalisun Tarayya 24 Sannan ga wasu ‘Yan Majalisun Jiha Su 40 Na dab da Faduwa Saboda Zalinci da Butulcin daka yiwa ‘Yan Tsohuwar PDP Domin babu yadda za’ai Su kai Labari tunda Jam’iyyar PDP a Halin yanzu batada Dan Takarar Gwamna Kamar yadda Kotu tayi Hukunci, Hukumar zabe ta INEC ta karba, Duk da naji Wata kotun a Kaduna tayi Umarnin a dakata tayi nata Hukuncin bayan zabe. Hakan zai hana Kanawa yin Asarar Kuri’ar su ta Hanyar zaben Dan Takarar da bazai iya tsallake Kotu ba.

A Karshe nasan zaka yarda Dani Madugu Kai ne Jagoran Butulci. Marigayi Alh Abubakar Rimi, Mai Girma Ambassada Aminu Wali, Alh Musa Gwadabe, Dauda Dangalan, Sanata Hamisu Musa Har ma da Marigayi Engr. Magaji Abdullahi Sun isheni Shaida.

Nagode Nine Naka:
Comrade Muzakkir Rabiu

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.