(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Murnar Lashe Zaben Buhari: Matashin daya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja domin taya Buhari murna

Karatun minti 1

Wani matashi dan shekara 25 mai suna Tukur Aliyu, ya fara tattakin nuna murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu, daga jihar Kebbi zuwan birnin Abuja.

Matashin dan asalin garin Kebbi yace ya shirya yin wannan tattaki domin cika alkawari daya daukar wa kanshi idan har shugaba Buhari ya sake lashe zabe a karo na biyu.

“Na shirya wannan tattaki ne badan komai ba sai da alkawarin dana dauka idan shugaban ya samu nasara ko bai samu ba a zaben 2019, kuma inayi ne don rajin kai na da kuma jami’iyya ta ta APC.”

Kafin fara tattakin matashi Tukur, ya bayyanawa kafafen yada labarai domin su san da tafiyar tashi.

A tare da Tukur akwai ‘yar karamar jakar goyo dake dauke da garin rogo kwana 1, siga, kosai da kuma ‘yan kudaden da basu gaza N1,500 ba.

Daga karshe yace yana fatan samun ganin shugaba Muhammadu Buhari domin ya taya shi murna baki da baki.

Tsakanin Kebbi da birnin Abuja akwai nisan kilometer 474.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog