Copyrighted.com Registered & Protected

Adamawa: Ganduje, El- Rufa’i na shirin kawo ‘Yan Sara-Suka domin tafka magudi – PDP

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Jami’iyyar PDP reshen jihar Adamawa, ta zargi jami’iyyar APC wajen shirin da take na dauko hayar ‘yan daba daga garuruwan Kaduna da Kano, domin yin amfani dasu wajen tada hankula a wajen zabe.

Jami’iyyar PDP ta fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren jami’iyyar na jihar Adamawa, Barrister Tahir Shehu inda yace labarin shirin babbar jami’iyyar na aiki da ‘yan daban ya iske su.

“Muna da labari daga majiya mai tushe cewa Gwamna jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i tare da Gwamman Kano, Dr Abdullahi Ganduje sunyi wa jami’iyyar APC alkawarin kawo musu daukin ‘yan Sara-Suka, domin taimakawa wajen yin karfa-karfa ko ta halim kaka na tabbatar da samun nasarar jami’iyyar a zaben sa za’a sake yi gobe Alhamis.” -Kamar yadda sanarwar ta fito.

Daga karshe sunyi kira ga al’umnar yankunan da za’a sake zabe, da su kwantar da hankalinsu, su fito suyi zabe ba tare da fargaba ba.

A nasu bangaren, jami’iyyar APC tayi Allah wadai da furucin jami’iyyar PDP, tace daga bangarenta babu wani abu mai kama da haka.

 

 

A kokarinmu na kawo labarai na gaskiya.

Jaridar Daily Trust, The Sun da sauran wasu manyan jaridun Najeriya sun rawaici wannan labari.

%d bloggers like this: