Ganduje ya kori Salihu Tanko Yakasai ‘Ɗawisu’

Karatun minti 1
Salihu Tanko Yakasai

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar ya sallami Salihu Tanko Yakasai daga mukaminsa na hadiminsa a kafofin yada labarai.

DABO FM ta tattara cewar gwamnatin ta sanar da korar Yakasai ta hannun kwamishinan yada labaran jihar, Mallam Muhammad Garba.

A dai ranar Juma’a ne dai Salihu ya yi kakkausan furuci a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, har ma ya ce gwamnatin APC a kowanne mataki ta gaza samar da zaman lafiya, wanda shi ne babban makasudin zabarta.

Kalaman da ba su yi wa magoya bayan APC da gwamnati shugaba Buhari ba.

Yanzu haka rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kama Salihu Tanko Yakasai a hanyarsa ta zuwa shagon aski a birnin Kano.

Ana zargin jami’an DSS da kama shi, sai dai jami’an su karyata hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Nigerian.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog