Daukar Nauyi: Ginshikin Talakawan Soba, Hon Ibrahim Hamza ya kafa tarihi

dakikun karantawa

A Litinin nan, 27 ga watan Yunin shekara ta 2020 Dan majalisar wakilai na Kasa mai wakiltar mazabar karamar hukumar Soba ta Jihar Kaduna Hon Ibrahim Hamza Soba, wanda aka fi sani da Ginshikin Talakawa. ya yi bukin kaddamar da ba da motoci 8 babura samfurin Bajaj da Classic 155 da keken guragu 70 ga wasu daga cikin al’ummomin mazabar tasa.
Taron da ya gudana a firamaren Soba, ya ga dumin al’umma magoya bayan Jama’iyyar Apc da ma sauran al’ummar karamar hukumar.

Da yake jawabi wurin kaddamar da bada tallafin, Dan majalisar Hon Ibrahim Hamza Soba ya ce, tun da aka zabe shi a shekarar 2019 a matsayin wakili a majalisar Kasa, ya ke kokarin samar da ababen more rayuwa ga al’ummar sa da nufin su amfana da wani hasafi na romon damakoradiyya. Kuma zuwa yanzu abun da ya aiwatar yana da amannar kwalliya tuni ta fara biyan kudin sabulu.

Ya ce, ko a kwanakin baya, ya raba abinci ga mabukata wanda daruruwan al’ummar karamar hukumar suka amfana.
Baya ga tallafin karo karatu da daliban karamar hukumar suka amfana a baya, yanzu kuma akwai wasu hazikan dalibai ‘yan asalin Soba da za su tafi kasar waje karo karatu saboda bajintar da suka nuna a baya.

Hon Ibrahim Hamza, ya kara da cewa, tun bayan zaben sa, ya yi kokarin habbaka sha’anin siyasa inda ya jawo kowwa a jiki ba tare da nuna ban-banci ko bangaranci ba, kuma har yanzu a haka ake a karamar hukumar.

Sai ya naimi wanda za su amfana da tallafin motoci da babura da ma keken guragun, su sa a ran su cewa Allah ne ya tsaga da rabon su. Kuma da yardan Allah wannan farawa aka yi.
Ya yi kira ga al’ummar mazabar sa, su kara hakuri kuma su cigaba da yiwa shuwagabanni addu’a da fatan Alheri.

Da yake nashi jawabin, Hakimin gundumar Soba Kuma Uban Garin Zazzau Alhaji Muhammad Bashir Shehu Idris, ya mika godiyar sa ta musamman ga Dan majalisa Hon Ibrahim Hamza Soba, a madadin al’ummar sa, Kuma ya yi kira da ya cigaba daga abun da ya faro na Alheri.
Alhaji Bashir Shehu Idris, ya kuma mika kokon baran al’ummomin da ibtila’in ambaloyar ruwa ta shafa a garin Maigana da Soba ga Dan majalisar kuma ya yi fatan su ma a kawo masu tallafi.

A jawaban su daban-daban, wasu daga cikin wanda suka amfana da tallafin sun yi matukar godiya da fatan Alheri ga Hon Ibrahim Hamza kuma suka yi alkawarin daurawa a kan kokarin da suke da shi domin cigaban siyasan gidan Ginshikin Talakawa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog