Surutanku ba za su hana mu cigaba da ayyuka a Kano ba – KNSG ga Kwankwasiyya

Karatun minti 1
GANDUJE
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje (APC)

Gwamnatin jihar Kano ta ce babu abinda zai hana ta ciwon bashi domin aiwatar da ayyuka a jihar Kano.

Kwamishinan yada labaran jihar, Mallam Muhammad Garba ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a matsayin  martani kan mika gwamnati zuwa kotu da kungiyar Kwankwasiyya ta yi a yau Litinin.

Kungiyar ta ce bai kamata gwamnatin jihar ya ciyo bashin Naira biliyan 300 da take son yi ba.

A cikin sanarwar da DABO FM ta samu, gwamnatin jihar ta ce babu gudu ba ja da baya a kan ciwo bashin, hasali ma, wadanda za su bayar da bashin sun amince da fitar da kudaden, sai dai tana jiran sahalewar Majalissa da hukumomin gwamnatin tarayya kan fara shirin karbo kudaden.

Kazalika gwamnatin ta ce kudirinta na yin layin dogo yana nan daram, babu gudu ba ja da baya.

Gwamnatin ta ce matsayin da Kwankwasiyya ta dauka ba abin mamaki bane, domin a cewarta ‘Kwankwasiyya ba ta ganin ayyukan alheri da gwamnati take yi a jihar Kano.”

Ta ce “bisa ayyukan da gwamnatin take yi, Kwankwasiyya tana fargabar gwamnatin Dr Ganduje za ta dusashe haskenta.”

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog