Kadan ma aka gani – Cewar Mai Mala Buni dangane da komawar Dogara zuwa APC

Karatun minti 1

Shugaban rikon kwaryar jam’iyya mai mulki a kasa, Mai Mala Buni ya bayyana cewar ‘yan Najeriya za su sha mamaki sosai nan gaba dangane da wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa da za su dawo cikin komarsu.

Hakan na zuwa ne a lokacin zantawarsa da sashen Hausa na BBC, in da ya jaddada cewar shirin da suke yi na karkashin kasa don ganin sun kara APC karfi, zai zowa da dama daga cikin ‘yan mamaki. Domin akwai da yawa da za su shigo tafiyarsu. Ya haskaka cewar dama da yawa daga cikin wadanda suka bar tafiyar a baya, wata damuwa ko bacin rai da sabani ne ya kawo hakan. Amma yanzu su na kan tuntuba da Kuma sulhunta membobinsu da dama wadanda ba sa ciki.

Da aka tambayeshi dangane da lagon dawowar tsohon kakakin majalissar wakilai ta kasa, tamkar wani coge ne don samar da wanda zai yi wa musulmin kudu takarar shugaban kasa, wato mataimaki, don ganin sun yi nasara a zabe mai zuwa na 2023? Sai ya kada baki ya ce, su yanzu ba zaben shugaban kasa ne a gabansu ba, na gwamnoni ne.

A nazirin masana,  ba shakka akwai kamshin gaskiya a game da wannan kulli da aka fara yi tun da hantsi. “Don ba makawa, idan ba wani yanayi ba, to APC za ta iya tabbatar da takarar shugaban kasa daga yankin kudu, musamman daga bangaren yammaci”, a cewarsu

Karin Labarai

Sabbi daga Blog