(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira miliyan 500 don yakar Malaria

Karatun minti 1
Dr Abdullahi Ganduje
Dr Abdullahi Ganduje

Gwamnatin jihar Kano tace ta kashe kudade sama da Naira miliyan 500 daga shekarar 2016 zuwa 2018 a kokarin ta na yakar cutar cizon sauro a jihar.

Kwamishanan lafiya na jihar Kano, Dr Kabir Getso shi ne ya bayyana haka a wani taron ranar Cutar cizon sauro ta duniya na shekarar 2019.

Yace an kashe kudin ne ta hanyar rabon magunguna, gidajen sauro ga mata masu juna biyu da sauran bukatu.

“Ya na mahimmaci asan cewa daga shekarar 2016 zuwa 2018, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Ganduje, ta samar da kayyaki na sama da miliyan 500 domin kawar da cutar cizon sauro a Kano.”

“Duk a cikin kudin, gwamnatin ta raba kayayyakin gwaje-gwaje zuwa ga kananan hukumomi 44 a jihar Kano.”

“Kayayyakin sun kushi magungunan yaki da cutar Malaria, kayayyakin gwaje-gwaje, rabawa mata masu juna biyu maganin cutar kyauta, Na’urar Microscope da Gidan Sauro mai dauke da magani.”

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa; Kwamishinan ya kara da cewa; Gwamnatin ta dukufa wajen kula da lafiyar mata da yara musamman mata masu juna biyu da kananan yara.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog