Siyasa

Har ‘Yan Boko Haram ‘yan APC suka zama don su rubutawa kansu kuri’a- Buba Galadima

Shugaban R-APC, kuma daya cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar, Engr Buba Galadima yace sun kammala dukkanin shirun da suka shirya domin dawo da zaben da aka kwace musu na shugabancin kasa a zaben 2019.

A wata ganawa da Buba Galadima yayi bayan fitowarshi daga kotu koli inda suka shigar da kara akan anyiwa Atiku Abubakar karfa-karfa wajen kwace zaben da Buba Galadima ya kira da zaben rashin adalci.

“Alhamdulillah, mun kammala nazarinmu, na shigar da kara a kotu, wannan kara mun tabbata cewa muna da shaidu na fashi da makami da jami’iyyar APC da mukarrabanta sukayi, kamar su hukumar zabe, ‘yan sanda da Sojoji. Idan dai akwai gaskiya da adalci babu abinda zai hana muyi nasara.”

“Kamar yadda kowa ya sani a  Najeriya dama duk duniya, ba’ataba yin zabe wanda akayi amfani da karfin tuwa ba har a hana jiha baki daya jefa kuri’a. “

“Kasan har ‘yan Boko Haram ‘yan APC suka zama, suna tada Bama-Bamai, suna sa motoci suna  harbe mutane don su samu damar  rubutawa kansu kuri’a. Toh Allah ya kama su, gashi yau rigar me gari ta bata.”

“Zamu kwaci mulkinnan a Kotu, saboda mune muke da kuri’u mafi yawa a zaben da akayi.”

Yace suna da tabbacin cewa kotu zatayi musu adalci indai za’a saka tsoron Allah da kuma yin abinda doka ta tsara a aiwatar.

Daga karshe Engr Buba Galadima yace akwai jihohin da jami’iyyar APC ta lashe amma duk ba’ayi amfani da na’urar Card Reader ba.

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Jami’an tsaro sun cafke Buba Galadima

Dabo Online

Halayyar Buhari ta gaskiya ta bayyana bayan darewarshi shugabancin Najeriya – Buba Galadima

Muhammad Isma’il Makama

Nafi gwamnatin Buhari amfani a wajen talakawa da al’ummar Najeriya – Buba Galadima

Dabo Online

Na zabi Kwankwaso a zaben fidda gwanin APC na 2015 don nasan yafi Buhari chanchanta – Galadima

Dabo Online

Bana bukatar sasantawa tsakani na da Buhari – Buba Galadima

Dabo Online

Zaben2019: Idan Ubangiji ne zai kirga kuri’u babu yadda Buhari zai iya cin zabe – Buba Galadima

Dabo Online
UA-131299779-2