Zaben Kano: Takai yace a zabi Ganduje – Salihu Tanko Yakasai

Dan takarar Gwamna jihar Kano karkashin Jam’iyar PRP, Mallam Salihu Sagir Takai ya yi kira ga magoya bayan shi da su zabi  Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na Jam’iyar APC a zaben karashe na gwamna da zaa gudanar ranar asabar, 23 ga watan Maris.

 

Mataimakin gwamnan jihar Kano a fanni yada labarai, Salihu Yakasai yace Mallam Takai ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayan sa a jiya.

Ya shaida musu cewa Gwamna Ganduje ya nemi shi sun tattauna kuma sun cin ma masakalar cewa wannan shine zai zamanto alheri ga jihar Kano.

TALLA

Kuma ya kara da cewa akwai kyakyawar alaka mai karfi tsakanin sa da Ganduje.

Masu Alaƙa  Bulama, ya bukaci EFFC ta bayyanawa duniya gaskiyar data gano akan bidiyon Ganduje

Dan haka yake kira ga magoya bayan sa na Jam’iyar PRP da su fito kwansu da kwarkwata domin su kadawa Gwamna Ganduje kuri’un su a ranar asabar mai zuwa, 23 ga watan nan.

Mallam Takai ya samu kuri’u kimanin dubu dari wato 100,000 a zaben da aka yi a baya, kuma yawan kuri’un da zaa jefa a zabe mai zuwa adadin wadanda suke katin zabe a gurin ya kai kimanin dubu dari da arbain Sato 140,000.

 

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: